Wani dattijo dan shekara 72 ya rasu a cikin jirgin sama a hanyarsa ta zuwa Abuja

Wani dattijo dan shekara 72 ya rasu a cikin jirgin sama a hanyarsa ta zuwa Abuja daga garin Kalaba na Jihar Kuros Riba.

Advertisements
Advertisements

Mutumin mai fama da ciwon shanyewar barin jiki na cikin jirgin kamfanin Air Peace ne a kan hanyarsa ta zuwa asibiti, rashin lafiyarsa ta yi tsanani a sararin samaniya.

Mai magana da yawun kamfanin Air Peace, Stanley Olisa ya ce da saukar jirgin Abuja, “mun yi gaggawar sanar da jami’an lafiya a filin, wadanda suka tabbatar da rasuwarsa, sannan suka tafi da sauran fasinjojin zuwa asibiti domin cika sauran ka’idojin da suka dace.

Stanley Olisa ya ce sai da aka tabbatar cewa mara lafiyan na iya yin tafiya a jirgi kafin a dauko shi.

Related Post

“Ma’aikatan lafiya a filin jirgi na Kalaba sun tanance sannan suka bayar da izinin daukarsa a jirgi; ammma kuma jikin nasa ya yi tsanani bayan tasowar jirgin.

“Air Peace riga ta yi feshin magani yadda ya kamata a jirgin kuma yanzu lamarin na hannun jami’an lafiya”, inji shi.