Sallah: Shugaba buhari yaja kunnrn mutane a filin idi yau da safe

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gudanar da Sallar Idi a fadarsa domin yin biyayya ga tsarin kula da lafiya sakamakon annoar korona.

Advertisements
Advertisements

Shugaban ya kuma yi layya kamar yadda addinin Musulunci ya bukata.

Tun da farko a sakonsa na Sallah ga ‘yan kasar, Shugaba Buhari ya yaba wa Musulmi da Kirsita bisa hakurinsu a wannan lokaci na cutar korona.

Sakon, wanda kakakinsa Garba Shehu ya aike wa manema labarai, ya ambato shugaban na Najeriya yana yaba wa “Musulmi da Kirista saboda bin dokokin kare kai daga kamuwa da COVID-19 don ya zama riba ga dukkan al’umma.”

  'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Hudu a Kaduna

“A bangarenmu, za mu ci gaba da fito da hanyoyin da za su sauwakawa mutane radadin da suke ciki sanadin wadannan dokoki,” in ji Shugaba Buhari.