“Ina kyamar kashe-kashen da akeyi” inji Rahama Sadau

Fitaccciyar tauraruwar fina-finan Kannywood, Rahama Sadau, ta yi Allah-wadai da rikicin da ke faruwa a Kudancin Kaduna.

Advertisements
Advertisements

Tauraruwar, wacce haifaffiyar jihar Kaduna ce, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su tattabar da zaman lafiya a yankin na Kudancin Kaduna.

“Ina kyamar kashe-kashen da ake yi a Kudancin Kaduna. Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha su tabbatar da zaman lafiyar dukkan ‘yan Nijeriya,” in ji ta a sakon da ta wallafa a Twitter ranar Talata.

Bangarorin al`umma da ke kudancin jihar na ci gaba da ɗora wa juna alhakin rikicin da ya ƙi ya ƙi cinyewa a yankin, wanda kuma ke haddasa asarar rayuka da dukiyar jama`a.

  Muslim Lawyers are warned not to defend the sentenced Kano singer

A halin da ake ciki, gwamnati ta kafa dokar hana fita a wasu ƙananan hukumomi biyu da nufin magance matsalar.

Amma masana harkokin tsaro na ganin cewa aiwatar da shawarwarin da wasu kwamitocin bincike suka bayar a baya, itace sahihiyar hanyar dawwamar zaman lafiya a yankin.