Wani dan sanda ne ya dakatarda da wani direba akan titi, ya karbi takardun motar bayan ya kamala bincike kuma takardun sun kamala sosai babu inda zai samu cin hanci sai yace ga takardun ka direban ya karba cikin murmushi yace nagode ranka shidade dan sandar bai kale shi ba sai ya qarayin murmushi wannan karon harda dariya.
Sai dan sandar ya dubi bakin direban sai yaga ashe wawulo ne irrin na Shagiri Girbau sai yayi maza yace stop !!!
Stop !!!
Kana tukin mota alhalin hakoranka basu cika ba ?? baka san cewa idan kana tuki kana dariya zai iya daukar hankalin sauran direbobbin dake kusa dakai ba ??
Kuma hakan zai iya janyo mumunnan hadarin mota idan baka sani ba !! lallai ya zama dole police tayi aikin ta zamu cika tarar naira 5,000 domin razanarda al’umma da kayi da kake cikin yi da kuma Zaka yi nan gaba
You must log in to post a comment.