Harkan shaye-shaye a duniya takai makura ta inda ake wasan boye da masu shaye-shaye da yan sanda a kowane sa’i a kowane lungu da sako na najeriya’
A kowane taron addini a masallatai da chochi, akan hanya kasuwa da gurin dabdalae jama’a se anyi hannunka me sanda ko kuma gaba gadi akan gargadi da a dena shaye-shaye,
A wani Bidiyo da Fugitive news tayi karo dashi a tiwiter, na nuni da wani saurayi ke marisa sakamakon shaye-shayen da yayi kafin karasowa wajen bikin aure.

Wani bawa Allah me suna @bb_ajiya ya wallafa a shafinsa tare da gargadin ko in damu yake cewa “ku dena shan wiwi amma kunki ji dan ku kalle shi”
Hakan abin kunya ne, ba kuma abin birgewa bane ahakan na kasan cewa ga me hankali.
Wa iyazubillahi, ya zamo ruwan dare mata da maza hakan ba wani abun mamaki bane kaga yarin ya rike da sigari, wiwi, kwaya ko giya, hakan ya zamo ado agaresu, duk haduwar gaye ko gayiya idan bata/baya shan daya daga ciki to tsami ne ma’ana sakarai ne ko kuma be san ciwon kansa ba
Daya daga cikin masu fada aji dake cikin malam kano yana yawanta da tsawaita gargadi akan abar shaye-shaye domin illar da shan yake dashi amma kullin kamar kara iza jama’a akeyi akan suje suyi tayi.
Daga karshe a koda wane lokaci bayan ya kammala gargadin yakan yiwa najejiya da mutanen cikinta addu’ar neman kariya daga ubangiji.
You must log in to post a comment.