Tagwaye Sun auri Tagwaye sun kuma haifi Tagwaye a rana daya

Wani hoto da ya karade kafofin sada zumuntar zamani na ‘yan biyu na rike da tagwayen da suka haifa a rana daya ya janyo cece-kuce

Advertisements
Advertisements

An gano cewa sunan tagwayen Sa’ad da Sa’id kuma sun yi aure a rana daya

https://www.youtube.com/watch?v=jaRRIH6X0IM
poton tagwayen kenan yayinda suke rike da yayan su suma duk tagwaye abin shaawa

Hotunan masu matukar bada mamaki sun bayyana inda kowannensu ke dauke da tagwayensa

Wasu hotuna masu matukar bada mamaki na tagwaye maza da suka yi aure rana daya ya bayyana.

Tagwayen sun aura mata tagwaye a rana daya kuma sun haifi tagwaye kowannensu a rana daya.

  Ministan Fasaha Yace Za'a Koyawa mutane 13,000 Aikin Yi

‘Yan biyun maza masu kama daya an gano sunayensu Sa’ad da Sa’id kuma an ga hotunansu dauke da jariransu.

A yayin da Legit.ng bata tabbatar da sahihancin labarin da ya bayyana tare da hotunan mazan da ‘ya’yansu ba, hotunan sun ci gaba da bai wa jama’a sha’awa.

A hotunan masu matukar bada sha’awa da suka karade shafukan sada zumuntar zamani, sabbin iyayen sun rike kyawawan ‘ya’yansu cike da kauna.

An gansu su kansu sanye da kaya iri daya da kuma huluna iri daya.

A hoton, dukkan tagwayen na zaune rike da tagwayen inda aka saka musu kaya iri daya.

Legit.ng ta ci karo da kyawawan hotunan ne bayan da wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna Oviesheikh ya wallafa hotunan a shafinsa.

  Kannywood: Dalilin dayasa na daina zagin kaina a film-Mai sana'a

Ya wallafa a shafinsa: “Tagwayen da suka auri tagwaye sun haifi tagwaye a rana daya.”

A wani labari na daban, wata irin soyayya mai rikitarwa ta ratsa wasu iyalai a kasar Rasha.

Tsohuwa mai shekaru 75 ce ake zargi da kwace saurayin diyarta bayan diyar ya ci amanarsa.

Mahaifiyar da diyar sun yi mugun fada mai cike da al’ajabi saboda saurayin.

Shi kuwa babu kakkautawa ya koma wurin tsohuwar mai shekaru 75.

Matar mai suna Galina Zhukovskaya tana zama a St Petersburg a yankin yammacin Rasha na Leningrad Oblast.

Ta aure tsohon mijin diyarta a 2010 bayan sun kulla alaka sakamakon cin amanarsa da diyarta take yi.

  Bayanan cika Shekaru 60 da 'yanci kai Buhari ya tabbatar da tabarbarewar tattalin arziki da tsaro a Najeriya

A lokacin da diyarta ta rabu da mijin nata, ta bai wa mijin matsuguni a gidanta wanda daga hakan soyayya ta kullu har suka yi aure.