Bazaai sallar idin babbar salla ba a wannan shekarar Kamar yadda me girma gobnan jihar Jigawa Badaru Abubakar ya fada.
Gobnan ya fada cewa duk wannan matsin da takurar da ake wa mutane ta samo asali ne akan kokarin da gobnati takey wajen yaki da cutar Coronavirus da ta addabi mutane ko ina.
A bisa wannan dalilin ne me girma gobna ya soke Sallar idi, bikin salla da kuma hawa da aka saba yi duk shekara ayankinsa.
Me girma gobnan ya bada umarni ga duk jamaan da ke kasarsa da su bi doka ayayin ganawarsa da yan jarida a Dutse jiya 21 ga watan yuli.
A cewar sa Jigawa ta riga ta fara samun nasara akan yakin da suke na kawar da wannan cuta da haka bazasu bari su bata rawarsu da tsalle ba dan haka ya soke idin bana na babba sallah.

Ya kuma kara da cewa dukda cewa yankunan arewa maso gabas basu kara tsintar wanda ya kamu da cutar ba na kusan wata daya kenan amma ya zama dole sukara kaimi domin ganin cewa sun kawar da ita a kina a fadin najeriya
Ya kuma ka jaddawa jama’a rayinsa yayinda suke tattaunawa da madaukin labaran gidan gobnati na jahar jigawar.
Gobnan ya kara da cewa ayanzu mutum daya ne ya rage musu a wajen da ake kebe masu cutar, wajen da ke fanisau da na birnin kudu duk an rufe saboda babu kowa a halin yanzu. Amma dai dukkansu lafiya suke saboda ko ta kwana.
A kaeshe gobna ya sanar da cewa kasuwanni da matattara jama’a sun kasance masu bin dokar nesa-nesa tin da dadewa hakan ya kawo raguwar yaduwar cutar a kasar sa.
You must log in to post a comment.