Hisbah: Auren wata budurw ya lalace sakamakon fitar wani diyonta da take lalata da wani a Sokoto

Hukumar Hisabah a Sokoto ta kama wani matashi da abokansa biyu a kan zargin yadda bidiyon tsiraicin wata yarinya da aka saka wa ranar aure a watan Oktoba

Advertisements
Advertisements

Daya daga cikin yaran da ake zargin ne ya yi lalata da yarinyar tun a 2017 a wani otel kuma ya nadi bidiyon ya ajiye na shekaru 3 sai daf da aurenta ya fitar da shi

Bayan fitar bidiyon, wanda za a daura wa aure da yarinyar ya ce ya janye kuma a halin yanzu yaron da abokansa da suka taya shi yadda bidiyon suna hannun hukuma

Hukumar Hisbah ta Jihar Sokoto a ranar Litinin ta tabbatar da kama wasu matasa uku da suka wallafa wani faifan bidiyo a kafafen sada zumunta yayin da ake yi wa wata yarinya mai shekaru 16 fyade.

  Buhari: Aikin banza Shuka dusa a ruwa-Taaziya

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa ana shirin daura wa yarinyar aure a ranar 17 ga watan Oktoba amma angon da ya ce ya fasa auren bayan fitowar bidiyon a kafafen sada zumunta.

Fitar da bidiyon lalata na budurwa ya saka ango ya fasa aurenta a Sokoto.

Kwamandan Hisbah na Jihar, Dakta Adamu Kasarawa, ya shaidawa ‘yan jarida a Sokoto cewa an mika babban wanda ake zargin, yaron wani da aka nada mukamin siyasa a jihar da abokansa biyu hannun hukuma.

Kasarawa ya ce hukumar ta kammala bincike a kan lamarin kuma za ta tabbatar an gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.

Mahaifiyar yarinyar da aka watsa bidiyon nata ta ce yaron da ake zargi ya bata yarinyarta ne tun a shekarar 2017 a lokacin shekarunta 16 shi kuma shekarunsa 17.

  Dakta Haruna Hamza ya Rasu Sakamakon Korona

Ta yi ikirarin cewa ya yi ajiyar bidiyon tsawon shekaru uku da nufin ya lalata wa ‘yar ta rayuwa.

“A ranar 20 ga watan Yunin 2020, an kira a waya daga Legas a kan cewa an ga bidiyon ‘ya ta wani Baffa Hayatu Tafida na lalata da ita.

“Wanda ake zargin ya aike wa wanda zai auri ‘ya ta bidiyon da kuma wasu mutane a shafukan sada zumunta,” in ji ta.

A cewarta, fitar wannan bidiyon ya saka wanda zai auri ‘yar ta ya ce ya fasa.

Mahaifiyar yarinyar ta yi ikirarin cewa mahaifin wanda ake zargin ya yi kokarin biyan ta kudi domin a kashe maganan kuma ya yi mata barazana da ta ki amincewa.

  Wani Gomna a Najeriya ya bukaci abayar da damar rike bindiga

Da aka tuntube shi, Hayatu Tafida, mahaifin yaron da ake zargin ya lalata yarinyar ya ce ya san da maganar amma bai yi kokarin bata toshiyar baki ba ko yi wa rayuwarta barazana.