Hadarin mota yayi sanadiyyar konewar wasu samarin daktoci biyu yan katsina

Hadarin mota ya ritsa da wasu samari a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba, wasu abokai 2 suka tafka hatsari a hanyar Katsina zuwa Dutsin-ma

Hadarin mota ya ritsa da wasu samari a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba, wasu abokai 2 suka tafka hatsari a hanyar Katsina zuwa Dutsin-ma

Advertisements
Advertisements

Cikinsu, har da wani Likita mai suna Dr Sadiq Yahaya Zakka, tare da Abokinsa Auwal Shehu

Kamar yadda rahotonni suka bayyana, motarsu ta kama da wuta sai da tayi kurmus da samarin Wani mummunan lamari ya faru a titin Katsina zuwa Dutsinma a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba.

Wasu abokai 2 suka mutu bayan motarsu ta kama da wuta, inda suka kone kurmus.

Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 3pm lokacin da motarsu, kirar Toyota Camry ta kama da wuta.

Dr Sadiq Yahaya Zakka bai dade da gama karatunsa ba a wata jami’ar China, kuma yana ta shirye-shiryen zuwa bautar kasa, amma sai mutuwa ta dauke shi tare da abokinsa Auwal Shehu Danfaranshi.

Related Post

Matashin likita tare da abokinsa sun kone kurmus a hatsarin mota a Katsina.

‘Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 2, sun cafke ‘yan fashi a Sokoto Daya daga cikin wadanda suka yi hatsarin akwai wani matashi mai suna Fahad.

Amma bai mutu ba don yanzu haka yana asibiti ana kulawa da lafiyarsa.

An birne Danfaranshi a ranar Lahadi da safe, 6 ga watan Disamba, kamar yadda musulunci ya tanadar.