Gwamnatin Tarayya ta bayar da Odar bude dukkanin makarantun Najeriya baki daya

Gwamnatin tarayya ta bada umurnin bude dukkan makarantu a Najeriya

Advertisements
Advertisements

Minista Adamu Adamu ya sanar da hakan madadin gwamnati

Yanzu an baiwa dukkan makarantu masu zaman kansu damar budewa ranar da suka ga dama

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya sanar da umurnin bude dukkan makarantun Firamare, Sakandare, da jami’o’i a Najeriya.

Adamu ya sanar da hakan ranar Juma’a a hira da manema labarai a birnin tarayya Abuja, Premium Times ta ruwaito.

Ya bada shawaran cewa dukkan makarantun su bi ka’idojin da aka gindaya na bude makarantu da kwamitin yaki da cutar Korona PTF ta sanar.

Tuni dai Ministan Ilimin ya sanar da ranar bude makarantun gwamnatin tarayya a fadin kasar ranar 12 ga watan Octoba, 2020.

  Yanzunnan Fada ya Barke Tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas

“Amma jihohi da makarantu masu zaman kansu zasu iya budewa duk ranar da suka ga dama.” Yace

Jihohi da dama irinsu Lagos, Oyo, Kano da Enugu tuni sun sanar da ranarkun bude makarantunsu