Gwamnatin jihar katsina ta ceto kimanin mutane 103 a hannun miyagu

Gwamnatin jihar Katsina ta ceto akalla mutum 103 da aka yi garkuwa da su

Advertisements
Advertisements

Gwamnan jihar, Aminu Masari, ya bayyana cewa ba a biya kudin fansa don ceto mutanen ba

Masari ya kara da cewa said a jami’an DSS da na rundunar soji suka saka hannu wajen ceto mutanen

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a ranar Juma’a, 8 ga watan Janairu, ya bayyana cewa rundunar tsaro sun ceto mutane 103 da aka yi garkuwa da su.

Masari ya bayyana hakan ne a yayinda yake jawabi ga wasu daga cikin wadanda aka ceto a gidan gwamnati, Katsina.

“Hakan ci gaban shirin da aka fara da ceto daliban makarantar sakandare na kankara 344 ne.

  Makiyayin da yaso Auren Zahra Buhari kuma dagaske a ransa

“Mun ga damar kuma muna amfani da wasu masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ganin cewa mun yi amfani da damar da kuma dawo da tarin mutanen da aka yi garkuwa da su.

“Zuwa yanzu mun yi nasarar dawo da mutane 103 da aka yi garkuwa da su kuma har yanzu ana kokarin ceto wasu.

Muna yin haka cikin sirri, don tabbatar da ganin cewa babu wanda ya raunana sannan a dakatar da ci gaban garkuwan da mutane.

“Don haka, muna aikata hakan ne tare da rundunar soji, na yan sanda da na DSS.

  Bam ya tashi a Katsina,

“Ina iya baku tabbacin cewa ba a biya yan bindigan kudin fansa ba,” in ji shi.

Masaari ya bukaci mutanen da su dauki lamarin a matsayin kaddara daga Allah madaukakin sarki.

“Kun ga yadda aka ceto ku. Ba a biya kudin fansa ba.

Wannan ya isa ya nuna cewa addu’a na da tasiri, ku yi hakuri, Allah ya saka maku da alkhairi kan wannan wahalhalun da kuka shi,” in ji shi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa wadanda aka ceto sun kasance mata masu shayarwa da yara daga shekaru shida zuwa 16.

  Kannywood: Masallacin da Gabon ta gina ya jawo rigima

Rahoton ya kuma nuna cewa tsoho dan shekaru 70 da soja da wani dan sanda mai yaki da ta’addanci na cikin wadanda aka ceto.