Gwamnati ta Dakatar da Mukabalar da Zaayi da Sheikh Abduljabbar

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da mukabalar da ta yi shirin yi tsakanin Sheikh Abdul-Jabbar Nasir Kabara da malaman jihar Kano a ranar Lahadi.

Advertisements
Advertisements

Hakan ya biyo bayan umurnin da wata kotun Majistare da bada ne na dakatar da mukabalar bisa bukatar da wani lauya mai zaman kansa ya shigar a kotun.

Lauyan, Barrister Ma’aruf Yakasai ya ce yin mukabalar tamkar sabawa umurnin da kotu ta bada a baya ne na hana Sheikh Abdul-Jabbar yin karatu a Kano.

Wata kotun Majistsare da ke zamanta Gidan Murtala a jihar Kano ta bada umurnin dakatar da mukabalar gwamnatin jihar ta shirya yi tsakanin Sheikh Abdul-Jabbar da malaman Kano a ranar Lahadi 7 ga watan Maris.

Alkalin kotun, mai shari’a Muhammadu Jibrin ya yanke hukuncin dakatar da mukabalar sakamakon bukatar da wani lauya mai zaman kasan, Barrister Ma’aruf Yakasai ya shigar wa kotun.

Yakasai ya bukaci a dakatar da yin mukabalar ne saboda hakan ya saba umurnin da kotu ta bayar a baya na hana Sheikh Abdul-Jabbar yin karatu da saka karatunsa a kafofin watsa labarai na jihar Kano.

Mai shigar da karar ya ce bashi daman yin magana yayin mukabalar tamkar watsa karatunsa ne wadda tunda farko aka dakatar da hakan.

Gwamnatin jihar Kano ta bada tabbacin cewa za ta yi wa kotu biyaya inda kwamishinan sharia na jihar Kano, Barrister Musa Lawan ya sanar da cewa ba za a yi mukabalar da aka shirya yi a ranar Lahadin ba.

Lauyan Barrister Ma’aruf mai suna Barrister Lukman Auwalu Abdullah ya ce hukuncin da kotun ta yanke ya musu dadi.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa  Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi.

For more chat me on 07069531852 Ku

  Apostle Paul Yace Wani Gwamna Mai Ci Zai Mutu