Gwamnan Jihar Borno Zai Bude Makarantun Addini Guda 27

  • Gwamnan jihar Borno ya yi kudurin kafa kwalejin ilimin addinin Musulunci a fadin jihar.
  • Manufar kafa makarantun shine bada hoto ga malamai don inganta karatun almajiranci.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya nuna shirin gwamnatin jihar na kafa kwalejin addinin Musulunci da ke ba da difloma a kowace karamar hukuma 27 da ke fadin jihar.

Advertisements
Advertisements

Gwamnan ya bayyana shirin ne a jiya yayin bude taron jin ra’ayoyin jama’a na kwanaki uku kan cikakken gyaran tsarin koyar da ilimin addinin Musulunci na gargajiya.

Taron, wanda aka gudanar a babban dakin taro na gidan Gwamnatin jihar, ya tattaro adadin masu ruwa da tsaki wanda gudunmawarsu zai yi amfani wajen tsara tsarin aiwatar da tsarin koyar da ilimin addinin musulinci na gargajiya na.

Gwamnan, yayin da yake bayyana bude taron, ya ce gwamnatinsa na da shirin gina manyan kwalejojin Islamiyya guda 27, daya a kowace karamar hukuma 27.

Manufar makarantar shine samar da dama ga manya wadanda suka cancanta da cikakkiyar ilimin addinin Islama su yi karatun difloma a fannin ilimin zamani domin inganta karantar da Almajirai a tsangayoyi.

Ya bayyana cewa za a tsara manyan makarantun Musuluncin don su ma su kasance cibiyoyin bincike na Musulunci baya ga koyarwa da koyo.

Wani Daraktan Cibiyar Ilimin Alkur’ani, na Jami’ar Ado Bayero da ke Kano, Farfesa Ibrahim Muhammad, wanda ya kasance bako mai jawabi a taron, ya jinjina wa Zulum saboda mayar da hankali kan salon shugabancin da ya kunshi cikakken shiri.

A cikin takardar tasa, Muhammad ya bayar da tarihi mai nuna yadda tsarin almajiranci ya fara a arewacin Najeriya, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki a jihar da su ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryen da ake shirin yi.

  Abdul-Jabbar yayi batanci ga sahabbai sabanin tarbiyyar gidansu