Gangamin kwato yaran da aka Sace a Kankara

Gangamin kwato yaranda aka sace a GSS Kankara ya zamo karo na farko da talakawan najeriya mazauna arewacin kasannan zasu yi.

Advertisements
Advertisements

Alkawarinda Buratai yayi na cewa zaai magana dasu ya zamo gazawa ga gobnatin najeriya.

Hakan ne yasa dukkanin hausawa sukayi niyyar temakawa kansu da yardan ubangiji Allah.

Ya zamo cin tuwo akwarya wa dukkanin daukacin yan arewa hakane yasa kowa ya futa kuma aka dauki aniyar zuwa karbo yarannan.

Akwai madakata ukku zuwa hudu da kowa da kowa zezo a hadu domin zuwa karbo su to halin kaka ne.

Jagororin wannan tafiya sun bayya bukatunsu ga dukkanin wadanda keda muradin binsu da kuma temaka musu cewa su taho da shirinsu domin kare jini biri jini zaayi acan.

  Shaye-Shaye:Wani Saurayi Ya haukace a wajen biki

Sun kuma nuna bukatar su ta addua ga dukkanin jamaar arewa baki daya.

Ga mahadar kamar haka

1. Mutanen Katsina

Wadanda zasu taho daga yankin DAURA zasu hadu a garin KOZA

Wadanda zasu taho daga yankin KATSINA BIRNI da FUNTUA, za’a hadu garin SHARGALLE.

2. Mutanen Kano

Wadanda zasu taho daga KANO zasu hadu a garin DANBATTA.

3. Jigawa

Mutanen da zasu taho daga JIGAWA zasu hadu a garin KAZAURE.

Ga jaddawalin tafiyar nan Domin karin bayani