Ganduje: Jihar Kano ta ware kudade N83.5m don yiwa dabbobi rigakafi

Ganduje ya bayyana cewa, ta bada kwangilar yiwa dabbobi rigakafi

Advertisements
Advertisements

Gwamnatin ta ware makudan kudade domin ta karfafa harkar kiwo a jihar ta Kano

Manufar rigakafin zai zama inganta kiwo da karfafa sana’ar kiwo ga makiyayan Kano

A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da bayar da kwangilar Naira miliyan 83.4 don rigakafin dabbobi, The Nation ta ruwaito.

Yarjejeniyar ta hada da samar da kwalabe 8,250 na maganin rigakafin Bovine Pleuropneumonia (CBPP) da kuma kwalabe 20,000 na maganin rigakafin Peste des Petits Ruminants (PPR).

Shirin allurar rigakafin a duk fadin jihar, wanda zai fara nan da wasu makonni zai dauki shanu 800,000 da kuma kananan dabbobi miliyan 1 a kowace shekara.

  Covid-19: Almajirai 193 suka kamu da cutar coronavirus a Kano

Shirin allurar rigakafin za a aiwatar da shi ne ta hanyar shirin Bunkasa Aikin Noma da Makiyaya (KSADP), Kwararren Masanin Sadarwa Ameen K.

Yassar, wanda ya bayyana a wata sanarwa a ranar Talata.

Ya bayyana cewa allurar rigakafin zata taka muhimmiyar rawa wajen inganta karfin dabbobi don yaki da cututtuka da kuma kula da jin daɗi da samar da manya da ƙananan dabbobi.

Ya bayyana cewa ba a gudanar da rigakafin dabbobi a jihar Kano ba a cikin shekaru uku da suka gabata kuma a sakamakon haka, yawancin al’ummomin makiyaya a jihar na fama da asarar dabbobi sosai.

Kodinetan ayyukan na jihar, Malam Ibrahim Garba Muhammed, wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin hukumarsa, ya bayyana cewa an yi hakan ne don hana dubban iyalai makiyaya a daya daga cikin jihohin da suka fi yawan jama’a a Najeriya rasa ayyukansu.

  Tabdi jan! Gobnan Jigawa ya hana sallar Idi a yankin sa

A wani labarin, Sarkin Fulanin Abeokuta, Muhammad Kabir Labar a ranar Talata ya ce an kashe makiyaya 23 tare da kona gidaje kimanin 20 a rikicin kwanan nan a Jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi magana a taron masu ruwa da tsaki kan rikicin manoma da makiyaya a jihar.