Faduwar Gini Yayi Sanadiyyar Rasa Ran wasu maaurata da yayansu 4

Faduwar Gini Yayi Sanadiyyar Rasa Ran wasu maaurata da yayansu 4 a jihar Kebbi

Advertisements
Advertisements

An sanar da Faduwar wani gini da Yayi Sanadiyyar Rasa Ran wasu maaurata da yayansu 4 a jihar Kebbi

Ana ci gaba da jimamin mutuwar iyalan gida guda da gini ya ruftawa a ƙaramar hukumar Arewa da ke jihar Kebbi.

Lamarin ya faru ne a daren Litinin inda ginin ya faɗa wa iyalan gidan Malam Ɗantani yayin da suke bacci, sai dai babban ɗansu ya tsira kasancewar ba ya ɗakin lokacin faruwar lamarin.

Ɗan majalisar dokokin jihar ta Kebbi mai wakiltar ƙaramar hukumar ta Arewa, ya ce ginin ya rusowa mutanen ne sakamakon mamakon ruwan sama da ake zabgawa a yankin.

  Matashiyar Budurwa: Tana neman saurayin Aure, idan akwai me sha'awa

Ya ce ginin da suke ciki na laka ne, kuma ya yi rauni ne saboda yawan ruwan saman da ake fuskanta. Tuni dai aka yi jana’izar iyalen a ranar Litinin.

Sai dai babban ɗan ma’auratan ya tsira kasancewar ba ya ɗakin lokacin faruwar lamarin a ƙauyen Tungar Gyado.

Garba Muhammad Yeldu ne shugaban karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi, ya kuma yi wa BBC ƙarin bayani kan lamarin.

“Kafin su rasun ma har matar gidan ta shiga maƙwabta da su ma gininsu ya faɗi ta yi musu jaje, to komwarta gida kenan ita ma nasu tsautsayin ya same su.

Wannan layi ne

Garba Yeldu ya ci gaba da cewa: ”Sunan Adamu Giwa shekararsa 46, sunan matar Darajatu mai shekara 30, sai Musbahu mai shekara 12, sai Saudatu ƴar shekara shida da Nusaiba ƴar shekara sai kuma Ya’u ƴar uku.”

  Toh fa! Rigiji Gabji!!! Fada ya kaure tsakanin Gwamnan Bauch da na Ondo

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce babu wanda aka tono da rai a cikinsu lokacin da masu aikin ceto suka je wajen.

Ya ƙara da cewa kusan a yankinsa gaba ɗaya ba zai iya ƙidaya yawan gidajen da suka rushe ba. ”A wannan ƙauyen na Tungar Gyado kuwa babu wani gida da wani ɓangarensa bai rushe ba, ”amma a wannan gidan ne kawai aka samu asarar rai,” in ji shi.

Ambaliyar ruwan da ake fuskanta bana na janyo asarar rayuka a jihohin Najeriya da dama.

Hukumomin jihar ta Kebbi sun ce a ƙalla mutum 10 ne suka mutu a ambaliyar ruwan da ake fuskanta a jihar a baya-bayan nan, baya ga lalata amfanin gona na fiye da naira biliyan daya.

  SMEDAN & BOA Collaborate in Boosting the Nigerian Economy