Dr Hakeem ya caccaki Sirikar Atiku Abisa Shigar Banza da tayi a bikinta

Dr Hakeem
Advertisements

Dr Hakeem Baba-Ahmed, jigon APC a jihar Kaduna, yayi magana akan shigar diyar Ribadu ranar aurenta

Advertisements
Advertisements
Advertisements

Ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda yace shigarta ta sha banban da koyarwar addininta da kuma al’adarta

Ya kuma roki iyaye da kuma matasa da su daina kwaikwayon shigar yahudawa, wadda tayi karo da koyarwar Musulunci

Dr Hakeem Baba-Ahmed, jigon APC a jihar Kaduna, yace shigar auren Fatima Ribadu tayi hannun riga da koyarwar addini da kuma al’adarta.

Idan baku manta ba, shagalin bikin Aliyu Abubakar dan mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da diyar tsohon shugaban EFCC da akayi a Asokoro, Abuja ranar Asabar. ya samu halartar manyan baki.

  Dahiru Usman Bauchi, ya musanta goyon bayan Mailafia a kan ikirarinsa

Kyakyawar amaryar da ta gama Nigerian Turkish International College, dake Abuja a 2015, ta saka wata rigar amare wadda yanayin adonta na Dubai ne.

Hotunanta sun yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, inda musulmai suka yi ta sukar rigar, ana cewa bata dace da Musulinci ba.

Korafin sa an hakan

Dr Hakeem baba Ahmad

“Gabadaya bai dace da addini da kuma al’adarta ba,” cewar Dr Hakeem Baba-Ahmed.

Dr Hakeem ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Lahadi, inda yake rokon iyaye da kuma matasa musulmai akan daina kwaikwayon al’adun yahudawa.

Kamar yadda ya wallafa, “A yau ne naga hotunan bikin wata yarinya musulma, tayi shiga wadda ta saba da addini da kuma al’adar ta.”

Ya kara da cewa, “Irin haka yana tada min da hankali. Ina rokon iyaye da kuma matasa da su dena kwaikwayon al’adun da suka saba wa tamu.”

Ya kuma roki masu bin shafinsa da kada suyi wani tsokaci na batanci a wallafar nan tasa ko kuma zagi.

  Kannywood: Matashi Musa Abdullahi, ya canzo shiri akan Maryam Yahaya

Wani Harun Elbinawi yayi nasa tsokacin, inda yace, “A arewacin Najeriya, ana amfani da dokar shari’a ne akan talakawa.

“Suna zartar da dokar shari’ar musulinci ne akan talakawan arewacin Najeriya amma babu mai sabawa dokoki da tsarin addini kamar su.

“Sannan suna amfani da kalaman musulinci idan suna so su yaudari talakawa.”

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani- Kayode, yayi magana akan bidiyon da ya bayyana yana dukan matarsa, Precious Chikwendu.

Tsohon ministan yayi magana ranar Asabar akan bidiyon da yayi ta yawo a duniya wanda aka ganshi yana dukan matarsa, inda yace ya kama ta da namiji a gadonsu na sunna ne.

  Bayanan cika Shekaru 60 da 'yanci kai Buhari ya tabbatar da tabarbarewar tattalin arziki da tsaro a Najeriya

Fani-Kayode yayi maganar ranar Lahadi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Facebook akan al’amarin. Ya ce ya boye haukar matarsa na tsawon shekaru 7 ba tare da ya bayyanawa duniya ba.

Advertisements
Advertisements
Translate »
%d bloggers like this: