Daliba ‘yar Makaranta Mai Shekara 13 Tasami Juna Biyu

Daliba ‘yar shekara sha uku (13) ta sami juna biyu ta yadda take iya cigaba dazuwa makaranta ko yaya takeji?

Advertisements
Advertisements

Fatu ta bayyana cewa ba abu mai sauki bane kasancewa a makaranta dauke da juna biyu, amma ta dauri aniyar kamala karatunta

A watan da ya gabata ne aka kai gwamnatin Tanzania kara kan haramta wa dalibai ‘yan matan da ke da juna biyu da masu shayarwa zuwa makaranta.

Tana daga cikin kasashe kadan a duniya da suke tsaurara wannan haramci.

A shekarar da ta gabata ne, a kuma irin wannan watan, wata kotu ta umarci kasar Saliyo ta dakatar da wannan haramci.

Don haka ta yaya abubuwa suka sauya a wannan kasa da ke yankin Afrika ta Yamma?

Shekarun Fatu (ba sunanta na gaskiya ba) goma sha uku (13), kuma tana dauke da juna biyu na wata hudu. An yi mata fyade ne.

A cikin wannan shekarar, halin da ta ke ciki dai yana nufin barin ta makaranta, sannan zai iya kasancewa tabbas a yi mata auren dole.

A maimakon haka ta tsaya a kan burin da take da shi na ta ga cewa wata rana ta zama ma’akaciyar jinya.

A cikin watan Maris, kasar Saliyo ta janye haramci kan kan ‘yan matan ta suka samu juna biyu ko suke shayarwa yayin da suke zuwa makaranta, watanni uku bayan da kotun Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afrika ta Yamma (ECOWAS) – ta yanke hukuncin cewa hakan.

”nuna banbanci ne” kuma ya saba wa ‘yancin kananan yara kan samun ilimi.Kasar ta dade tana fama da matsalar daukar ciki a tsakanin kananan yara – fiye da kashi 35 bisa dari na ‘yan mata masu kasa da shekara 18 sun haihu a cikin shekara ta 2013.

Adadin ya karu – zuwa kashi 65 bisa 100 a wasu yankunan – lokacin barkewar annobar cutar Ebola a shekarar 2014 zuwa 2015 lokacin da aka tilasta rufe makarantu.

.

  Kannywood: Exclusive interview with Hadiza Kabara