Dakta Haruna Hamza ya Rasu Sakamakon Korona

Dakta Haruna Hamza ya rasu Sakamakon corona virus wacce aka fi sani da covid-19

Advertisements
Advertisements
  • Kafin rasuwarsa, Dakta Haroun Hamzat ya yi aiki a hukumar lafiya bai daya da ke karamar hukumar Orile ta Jihar Legas.

Obafemi Hamzat, mataimakin gwamnan Jihar Legas ya rasa kaninsa, Haroun, sakamakon kamuwa da cutar coronavirus da ya yi.

Kafin rasuwarsa, yana aiki ne a cibiyar lafiya bai daya da ke Karamar Hukumar Orile Agege da ke Jihar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar Likitocin Najeriya, NMA, reshen Jihar Legas ta ce tana cikin alhani bisa rasuwarsa.

“Ya yi aiki a matsayin jami’in lafiya a daya daga cikin cibiyoyiin lafiya bai daya a karkashin karamar hukumar Orile kafin rasuwarsa.

“Muna taya iyalansa, abokansa, abokan aiki da ma’aikatan PHC ta jihar Legas. Muna adduar Allah ya kiyaye ‘yan uwanmu daga irin wannan mutuwar ta masu karancin shekaru.

“Muna adduar Allah ya bawa iyalansa da dukkan mu hakurin jure rashinsa. Amen. Muna bankwana da dan uwan mu likita, Dakta Haroun Hamzat. Allah ya jikanka da rahama. Amin.”

A halin yanzu Najeriya na fuskantar annobar korona karo na biyu.

Shugaban hukumar, Magaji Rimingado, wanda ya bayyana haka ga yan jarida ranar Talata, ya ce daga 2015 zuwa 4 ga Janairun 2021, gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 7 a tsarin wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata, amma ana samun korafin daliban da suka rage a kasashen waje.

Ganin yadda korafe korafe suka yi yawa kuma ya kamata ace da yawa yawancin daliban sun kammala karatun su, gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar da tayi “bibiya”, bincika ta kuma dauki mataki akan badakalar”, in ji Rimingado.

  Yanzunnan Fada ya Barke Tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas