Buhari ya bayyana mahimman abubuwa 5 a bayan sabuwar shekara

Buhari ya yi jawabi ga al’ummarsa da safiyar Juma’a, 1 ga watan Junairu, 2021, Yayinda yan Najeriya ke murnan sabuwar shekara.

Advertisements
Advertisements

Shugaban kasan ya jaddada alkawuran da yayiwa yan Najeriya a jawabinsa, inda ya tabbatar da cewa lallai an ji jiki a 2020.

A jawabinsa, shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta farfado da tattalin arzikin Najeriya kuma za tayi yaki da cin hanci da rashawa.

Hakazalika ya yi alkawarin kare rayukan yan Najeriya da dukikoyiyinsu. Legit ta tattaro muku muhimman abubuwan da ya fada:

1. Ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro

Shugaban kasan ya jaddada cewa zai yi garambawul cikin lamarin tsaro a 2021.

  Mutanen da abin ya shafa un kulle hanyar Kaduna Zuwa Abuja||Zanga-Zanga

A cewarsa, za’a karawa Sojoji da yan sanda kaimi domin dakile yan bindiga a ciki da wajen kasa.

2. Jaddada niyyar cika alkawarin da ya yiwa matasan Najeriya

Shugaban kasan ya jaddada niyyar cika alkawura biyar da ya yiwa matasan Najeriya sakamakon zanga-zangan #EndSARS.

Ya ce gwamnatinsa ta saurari bukatar matasan Najeriya.

3. Tattalin arzikin Najeriya Shugaba Buhari a jawabinsa ya bukaci yan Najeriya su kwantar da hankulansu saboda zai farfado da tattalin arzikin kasar ta hanyar dauke hankalinmu daga man fetur zuwa aikin noma domin samun isasshen abinci.

Ya yi bayanin cewa wannan gwamnatin na ayyuka daban-daban domin samawa matasa aikin yi da taimakawa kananan yan kasuwa.

  A Duniya : Dalilai 10 da suka sa fim din yafi dukka Fina-finan Kannywood

4. Yaki da rashawa

Shugaban kasan ya kara da cewa Najeriya ta samu riba a yakinta da rashawa kuma a wannan sabuwar shekara gwamnatinsa zata kawar da rashawa.

5. Annobar Korona

Shugaba Buhari ya zayyana kokarin da gwamnatinsa tayi domin sayan rigakafin Korona ga yan Najeriya.

A cewarsa, gwamnatin ta lashi takobin kiyaye kasar da waiwayen annobar Korona ta biyu.