Boss Mustapha Yace Katin Shaidar Riga Kafin Korona Zai Zama Sharadin Fita Daga Najeriya

Boss Mustapha ya bayyanawa ‘yan Najeriya wajibcin yin allurar rigakafin cutar Korona.

Advertisements
Advertisements

Boss Mustapha yace da alamu nan gaba kadan allurar ta zama wajibi ga duk mai son fita wajen Najeriya.

Hakazalika ya bukaci ‘yan Najeriya da su saki jiki da allurar da cewa tabbas bata da wata illa Shugaban kwamitin yaki da kwayar cutar korona a Najeriya (PTF), Boss Mustapha, ya ce nan gaba katin shaidar yi wa mutum allurar rigakafin cutar zai zama wajibi ga matafiya kasashen waje.

 Mustapha wanda kuma shi ne sakataren Gwamnatin Tarayya, ya bayyana hakan ne a Fadar Shugaban Kasa a yau Asabar jim kadan bayan an yi wa shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo allurar rigakafin.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su kokarta domin yin rigakafin da zimmar kare kansu daga cutar, wadda tuni ta halaka mutum kusan 2,000 a kasar da adadi mai yawa a sauran kasashen duniya.

Tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya samu matsayi a jihar Kaduna Katin shaidar rigakafin korona zai zama sharaɗin fita daga Najeriya.

Yin dari-dari da allurar wajibi ne a daina shi domin kuwa maganar gaskiya ita ce, nan gaba kadan babu wanda zai fita daga kasar nan ba tare da ya nuna shaidar an yi masa ba.

Ban tabbatar ba, amma na ji tuni wasu kasashe suka fara dakatar da karbar baki, ciki har da na ibada, idan ba su da shaidar rigakafin.

Ya kara da cewa Shugaba Mhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo sun gabatar da kansu ne a fara yi musu rigakafin domin su tabbatar wa da ‘yan kasar cewa ba ta da wata illa.

Obasanjo yace Na kamu da COVID-19 amma ban ji alamar komai ba a jikina har na warke.

Buhari ya yi rigakafin ne da misalin karfe 11:51 na safe a wani takaitaccen bikin da manyan jami’an gwamnati suka halarta a dakin taro na New Banquet da ke Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Babban likitan kansa, Dr Shuaib Rafindadi Sanusi ne ya yiwa shugaban kasar allurar ta rigakafin, yayin da mataimakin shugaban kuma Dr Nicholas Odifre, likita na musamman ga mataimakin shugaban kasar.

For more info chat me on 07069531852

  Sallah: Shugaba buhari yaja kunnrn mutane a filin idi yau da safe