Boko Haram: Ya kamata a mayarda yan gudun hijira garuruwansu- Zulum

A cikin hira ta musamman da Gwamna Babagana Zulum na Borno ya yi da BBC Hausa, ya bayyana ra’ayinsa kan abubua da yawa ciki har da batun cire manyan hafsoshin tsaron ƙasar da wasu ‘yan ƙasar suke ta kiraye-kirayen yi.

Advertisements
Advertisements

Gwamnan jihar Borno da ke Najeriya, Babagana Zulum, ya shaida wa BBC Hausa cewa kungiyar Boko Haram tana ci gaba da daukar mutane domin su taya ta yaki.

“Gaskiya ne kungiyar Boko Haram na ribatar mutane domin su shiga cikinta kuma hakan kuma abin tsaro ne,” in ji gwamnan.

Sai dai Gwamna Zulum ya tabbatar da cewa “idan har jama’ar da ke sansanonin ‘yan gudun hijra a jihar Borno ba su samu abin da suke so ba musamman damar komawa garuruwansu domin noma to fa dole ne su shiga kungiyar Boko Haram.

“Mutane sun gaji da zama a sansanin masu hijra. Ba sa samun abin da suke so. Dole ne su koma garuruwansu domin samun damar yin noma da kiwo kasancewar babu wata gwamnati da za ta iya samar da ciyarwa gare su mai dorewa,” a cewar Gwamna Zulum.

Dangane da garuruwan da jama’arsu suka koma, Farfesa Babagana Umara ya ce sun samu nasarar mayar da mutane garuruwansu kamar Kukawa da Mafa sannan nan ba da jimawa ba “za mu mayar da mutanen Kawuri.”

“Amma muna fatan sojoji za su kara kaimi wajen ganin an mayar da al’ummar Baga da Marte da Malam Fatori da Guzamala”.

Yanayin tsaro a jihar Borno

Gwamnan jihar ta Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a wata hira ta musamman da sashen Hausa na BBC, ya ce yanayin tsaro a jihar tasa na bunkasa amma har yanzu akwai sauran rina a kaba kasancewar Boko Haram na maboyarsu.

Ya ce: “‘Yan kungiyar na fakewa a tafkin Chadi da kuma dajin Sambisa. Kuma idan har ba a bi su har ciki ba an kore su ba to fa akwai matsala. Korar su daga hedikwatarsu ita ce hanya guda daya ta kawo karshen Boko Haram.”

Sai dai kuma gwamnan ya ce shiga tafkin Chadi da Zambisa dole ne sai Najeriya ta samu hadin kai na gaskiya da kasashen tafkin na Chadi.

Dangane da tambayar da aka yi wa Gwamna Zulum ko akwai wasu wurare da kungiyar Boko Haram ke rike da su a jihar ta Borno? Sai gwamna ya ce ” gaskiya fisabilillahi babu wani yanki da ke hannun kungiyar Boko Haram, sai akwai yankunan da babu jama’a a cikinsu. Abin da nake nufi shi ne har yanzu jama’a ba su koma garuruwansu ba.”

Ya kara da cewa “wallahi kafin zuwan Shugaba Buhari yanayin tsaro a jihar Borno ya yi muni kwarai saboda a lokacin kananan hukumomi 20 ne a karkashin Boko Haram amma yanzu ba haka ba ne.”

Yaushe za a kare Boko Haram?

Da aka yi wa gwamna Babagana Zulum wannan tambaya, sai ya ce ” hanya daya ta kawo karshen Boko Haram ita ce tabbatar da alaka mai kyau tsakanin sojoji da farar hula.”

Ya kara da cewa “na sha magana cewa duk inda ka je za ka ga sojoji da ‘yan banga tare. Amma abin da nake cewa shi ne sojoji su bai wa farar hula kariya domin samun damar komawa gidajensu su yi noma.”

Farfesa Zulum ya kuma ce tabbas sojoji na iya bakin kokarinsu amma abin da ya “dame mu shi ne yaushe ne wannan yaki na Boko Haram zai kare.”

‘Abin da nake nufi da sojoji na yi min zagon kasa’

Related Post

A kwanakin baya ne dai aka kai wa gwamnan da tawagarsa hari a kusa da garin Baga inda rahotanni suka ce an samu wadanda suka jikkata a tawagar tasa.

Wannan ne dai ya sa gwamna Zulum ya bayyana cewa sojojin da ke yaki da kungiyar Boko Haram na yi masa zagon kasa.

Da BBC ta tambayi gwamna Zulum ko me yake nufi da zagon kasa? Sai ya ce “da farko har yanzu ban janye kalamaina ba. Ina kan bakata kan cewa ana yi min zagon kasa.

Amma dai ban kama suna ba. Ban ce shugaba Buhari ba. Saboda duk wani abu da za a yi ya haifar da cikas ga yaki da Boko Haram zagon kasa ne. Idan aka bayar da kudin makamai sai sojoji suka ki siya ka ga wannan ai zagon kasa ne. Kai hatta rashawar nan da ake fama da ita, ita ma ai zagon kasa ne.”

To sai dai gwamna Zulum ya bayyana harin da aka kai masa da cewa “abin kunya ne” kuma “ni ban ji tsoro ba saboda na dogara ga Allah domin babu abin da zai sami Musulmi sai da iznin Allah.

An kai min hari da bama-bamai kuma Allah ya tsallakar da ni. Dole ne mu daina tsoro saboda idan muna tsoro ta yakin nan ba zai kare ba.”

Ra’ayin Zulum kan cire hafsoshin soji

‘Yan Najeriya da dama na ta kiraye-kirayen ganin Shugaban Najeriya ya yi sauyi a tsarin tsaron kasar ta hanyar sauya manyan hafsoshin tsaron kasar.

Gobna zulum tare da yan jarida

To sai dai gwamna Zulum ya ce ” cire manyan hafsoshin tsaro ba abin da ya dame ni ba. Burina shi ne a samar da zaman lafiya a jihar Borno.”

Ya kara da cewa “Na hadu da shugaba Muhammadu Buhari amma ni ban yi masa wannan magana ba. Wannan dama ce ta shugaban kasa.

Tsarin mulkin Najeriya ya fayyace hanyoyin da shugaba zai bi domin yin nadi ko kuma sauyin hafsoshin tsaron kasa. Ni wannan ba abun da ya shafe ni ba ne. Shugaban kasa ne ke da wuka da nama.”

‘Ban ce ba zan nemi ta-zarce ba’

Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce “babu inda na taba cewa ba zan sake neman kujerar gwamnan jihar Borno ba.”

Ya kara da cewa ” ko lokacin da nake neman kujerar gwamna a karon farko sai da na nemi zabin Allah. Kuma Allah ya zaba min. A saboda haka yanzu ma sai na nemi zabin Allah.”

Dangane ne kuma da ra’ayinsa kan shiyyar da mulkin Najeriya ya kamata ya koma bayan shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023, gwamna Zulum ya ce “A yi adalci”.

A ranar Laraba ne dai kungiyar IS ta ce ta kashe sojojin Najeriya guda bakwai a garin Kukawa da ke jihar Borno a arewacin Najeriya, yayin da rahotanni suka ce kuma mayakan sun kuma yi garkuwa da mutane da dama a garin.