Boko Haram ta dauki nauyin duk wani kashe kashe da ake a arewa

Boko Haram ta yi ikirarin cewa ita ta kaddamar da kisan kiyashi a garin Zabarmari, Borno

Advertisements
Advertisements

A cewar wani kwamandan kungiyar, sun aiwatar da mummunan harin ne domin fansar mutanensu da sojojin Najeriya suka kashe

Ya kuma gargadi yan farar hula a kan su guji yi musu leken asiri ko su dandana kudarsu

Kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta dauki alhakin harin da aka kai garin Zabarmari na jihar Borno.

A wani bidiyo da ta saki a ranar Talata, kwamandan kungiyar ya yi jawabi a faifan inda ya bayyana cewa sun aiwatar da kisan kiyashin ne domin rama kisan mambobinsu da sojojin Najeriya suka yi.

  Wani Jajirtaccen Dan Najeriya Ya Kirkiri Kafar Yanar Gizo Gizo Saboda Rage Zaman Banza

Kungiyar ta gargadi yan farar hula da su guji yin leken asiri a kansu, shafin HumAngle ta wallafa a Twitter.

A ranar Asabar ne kungiyar yan ta’addan ta yiwa wasu manoman shinkafa kisan kiyashi inda ta kashe akalla mutane 43 a jihar ta Borno.

A halin yanzu, biyo bayan kisan manoma 43 a jihar Borno wanda yan Boko Haram suka yi, an bukaci gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar sauya tsarin tsaro a Najeriya.

Dr. Ahmad Lawan ya yi kiran ne a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, lokacin da ya jagoranci tawagar Shugaban kasa domin yi wa gwamnati da mutanen Borno jaje kan mummunan lamarin, jaridar The Sun ta ruwaito.

  Boko Haram: Sun kai mummunan hari a Borno

A cewar Lawan, tsarin da ake dashi a kasa baya aiki, inda ya kara da cewa gwamnati na bukatar samun sabbin manufofi da kuma ganin yadda tsarin tsaron zai inganta.

A gefe daya kuma, Garba Shehu, babban mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kafofin watsa labarai, ya ce kiraye-kiraye da ake yi na a sallami shugabannin tsaro baya kan layi.