Boko Haram Sunyi kacha-kacha da wasu manoma ba ji ba gani

Boko haram sunyi abinda baa so, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya aika da sakon ta’aziyya ga iyalan manoman da Boko Haram suka ka yi wa kisan a karamar hukumar Jere, jihar Barno.

Advertisements
Advertisements

Tuni dai aka yi jana’izar mamatan da safiyar lahadi.

Yadda Boko Haram suka kashe manoman shunkafa 44 a jihar Barno

Akalla manoman shinkafa sama da 40 wasu mahara da ake zaton Boko Haram ne suka yi wa kisan gilla a tsakiyar gonakinsu a daidai suna aikin girbi.

Dan majalisar Tarayya dake wakiltar yankin Ahmed Satomi, da aka kai wa hari ya shaida haka yana mai cewa zuwa yanzu an mika musu gawarwakin manoma 44 da aka yi wa kisan gilla a gonakin su, wanda za a rufe ranar Lahadi.

  Jami'ar BUK ta Gindayawa Dalibai da Malamai Dokoki Bayan Anbude Jami'ar

” Manoma da masu kamun kifi 44 da aka kawo mana gawarsu zuwa yanzu. Duka wadannan manoma na aiki ne a wani katafaren gonan shinkafa da ke garin Garin-Kwashebe.

Haka shima shugaban kungiyar Manoman shinkafa na jihar Barno, Hassan Zabarmari ya tabbatar wa PREMIUM TIMES aukuwar wannan mummunar al’amari.

Majiya mai karfe ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa saida maharan suka tattara manoman sannan suka rika bi suna kashe daya bayan daya dukkan su.

Idan ba a manta ba a wannan rana ne ta Asabar, ake zaben kananan hukumomi na jihar Barno, bayan an shafe shekaru 12 ba ayi zaben kananan hukumomi a jihar ba.

  Gangamin kwato yaran da aka Sace a Kankara