Boko haram: Mutan Borno sun dauki babban mataki akan kisan da akawa mutanensu

Boko haram sun jawo dalilin da yasa Jama’a sunyi saukar addu’o’i da Al-kur’ani a dalilin kisan wulakancin da akayi wa mutanensu.

Advertisements
Advertisements

Mutanen Borno sun taru a wani masallaci sunyi ta aika ruwan du’a’i iri-iri

Anyi saukar Kur’ani da kuma addu’o’i har fiye da kafa miliyan 40 a zaman da sukayi

Rahotanni daga BBC Hausa sun bayana cewa an samu wasu mutanen jihar Borno da suka hadu, suka yi addu’o’i domin kawo karshen rikicin Boko Haram.

Wadannan Bayin Allah sun yi addu’o’i fiye da miliyan 41 a jihar Borno domin Allah ya kawo masu maganin ‘yan ta’addan kungiyar nan ta Boko Haram.

  Yanzunnan Fada ya Barke Tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas

BBC ta ce kungiyar Borno Concerned Citizen ta mazauna Borno da suka damu da halin da jihar take ciki ne su ka gudanar da wannan taron addu’o’i a jiya.

A ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, 2020, aka yi wa ‘yan ta’addan ruwan addu’o’i a Maiduguri.

Wata daga cikin ‘yan kungiyar ta masu kishin jihar Borno, Zahra Maiduguri ta shaida wa manema labarai sun yi saukar Kur’ani da addu’o’i 41, 837,016.

Kamar yadda Zahra Maiduguri ta bayyana, Alaranmomi sun ja “Istigifari” 13,669,000 domin tuba ga Allah, sannan sun karanta “Ya Laɗifu’ kafa 10, 688, 000.

Bayan haka, an karanta Suratul Masad kafa miliyan 5, 259, 000 da Ayatul Kursiyy sau 7, 00 da Salatul Fatih kafa 38, 000 da ‘Ya Qahharu’ kafa miliyan guda.

  Kaduna State Students Kidnappers Make a Final Decision

An kuma karanta Suratul Kahf sau shida da wasu lakanoni irinsu Ya Salamu da Bismilla da Salatin Manzon Allah da sauran addu’o’i daga cikin Al-Kur’ani.

Ba a addu’o’i abin ya tsaya ba, wannan gungu da malamai da shugabannin al’umma sun kauda shanu aka zubar da jinanansu domin neman bukata wurin Ubangiji.

Wannan ya zo ne mako guda bayan an kai mugun hari a Zabarmari. Wannan hari ne yayi sanadin mutuwar manoma 43 ko 78 da aka yi wa yankan rago ana ji-ana gani.

Kun ji labarin yadda Boko Haram suka yanka wani Bawan Allah wanda Matar shi ta haihu, ya je neman masu abinci, daga nan bai dawo ba, sai dai aka kawo gawarsa.

  Yanzu Yanzu: Sojojin Najeriy sun kashe kwamandojin Boko Haram 7 a Chadi

Bayan mako guda da harin, Mai Garin Zabarmari ya yi hira da ‘yan jarida game da wannan hari.