Boko Haram: Dakarun Sojin Najeriya sun Fusata Kwarai akan kashe Kanal Bako

Najeriya
Advertisements

Dakarun sojin Najeriya sun nuna fushi kan wariya da aka nunawa sauran sojoji da suka mutu tare da Kanal Bako

Advertisements
Advertisements
Advertisements

Kanal Bako ya kasance kwamandan sashi 2 na Operation Lafiya Dole, rundunar da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar

Yan Boko Haram ne suka kashe kwamandan tare da wasu sojoji a harin bazata da suka kai masu Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi fushi sosai da mahukunta kan rashin karrama sauran sojojin da yan Boko Haram suka kashe tare da kwamandansu, Kanal Dahiru Bako, Sahara Reporters ta ruwaito.

Kafin kisan nasa, Bako ya kasance kwamandan sashi 2 na Operation Lafiya Dole, rundunar da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.

  Sojojin Najeriya sun koka cewa ba Kanal Bako kurin suka rasaba a harin da aka kai musu

Babban jami’in sojan ya rasa ransa a ranar Litinin, a wani harin bazata da yan ta’addan suka kai kansu, kamar yadda HumAngle ta ruwaito.

Babban kwamandan Boko Haram da matansa 4 sun mika kansu ga sojoji a Borno Ba Kanal Baƙo kaɗai aka kashe ba:

Sai dai an tattaro cewa ba a ambaci sauran sojoji uku da aka kashe tare da Bako ba balle a karrama su.

Sunayen sauran sojojin da aka kashe tare da kwamandan sune; Lance Corporal Oluwaseyi, Lance Corporal Nwobuji Desmond da Private Aliyu Ibrahim.

An ruwaito cewa babu wani sakon jaje daga hukumar sojin zuwa ga iyalan mamatan.

Wani makusanci, wanda ya zanta da HumAngle, ya bayyana cewa da hakan, hukumomin na ci gaba da nuna banbanci tsakanin wadanda ke karkashinsu da kuma gaza nuna jagoranci nagari.

  MC Tagwaye ya auri Maryam Uwais 'yar mai bai wa Buhari shawara

A baya mun ji cewa, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya yi wa Rundunar Sojin Najeriya ta’aziyyar rasuwar Kanar Dahiru Bako da ya mutu sakamakon harin kwantan bauna da Boko Haram suka yi wa sojoji a Borno.

Advertisements
Advertisements
Translate »
%d bloggers like this: