Boko Haram: Babban rashi a gidan Sojin Najeriya na Kanal D.C. Bako

Har yanzu mayakan kungiyar Boko Haram na kai hari jifa – jifa a kan rundunar sojoji a jihar Borno

Advertisements
Advertisements

Gwamnatin Najeriya ta shafe fiye da shekaru 10 ta na yaki da kungiyar Boko Haram mai ikirarin yakin Jihadi

Rundunar soji ta yi asarar manya da kananan dakarunta yayin yaki da mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno da sauran jihohin arewa maso gabas

Rundunar soji ta Najeriya ta sanar da mutuwar Kanal D. C. Bako, kwamandar runduna ta 25, wanda mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe a jihar Borno.

Ado Isa, kakakin rundunar atisayen Lafiya Dole, ya ce Kanal Bako ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wa tawagarsa harin kwanton bauna yayin da suka fita sintiri.

  Tirkashi! Anyi dumu-dumu da wani ango tare da kawar amarya a ranar biki

A cikin jawabin da Isa ya fitar ranar Litinin, ya ce Kanal Bako ya rasu a asibiti duk da ya fara nuna alamun farfadowa bayan harin ‘yan ta’addar.

Sai dai, Isa bai yi karin bayani a kan adadin sauran dakarun soji da su ka samu raunuka yayin harin kwanton baunar da aka kaiwa tawagar sojojin ba.

“Rundunar atisayen Lafiya Dole ta rasa jarumi, daya daga gwarazanta na yaki, Kanal DC Bako.

“A matsayinsa na kwamanda, kullum shine a gaba idan rundunarsa za ta fita aiki.

“Da irin wannan salon jarumta ne ya jagoranci rundunarsa zuwa yankin Sabon Gari – Wajiroko a Damboa domin kawar da sauran mayakan kungiyar Boko Haram a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba.

  Ibtila'in Gobara ya kona babbar kasuwar Doya a Filato baki daya

“Dakarun soji, a karkashin jagorancinsa, sun samu nasarar dakile harin kwanton baunar da aka kai mu su tare da samun nasarar kwace makaman ‘yan ta’adda.

“Sai dai, abin takaicin shine Kanal Bako ya samu munanan raunuka kasancewar shine a gaba yayin da sojoji ke yin musayar wuta da ‘yan ta’addar da suka kai musu harin kwanton bauna da misalin karfe 10:00 na safe.

“Kanal Bako ya fara farfadowa a asibiti bayan an yi masa tiyata, har ya samu damar yin Sallah da safiyar yau, Litinin, kafin ya rasu a asibiti.

“Mu na addu’a Allah ya ji kansa,” a cewar sanarwar da Isa ya fitar.