Bayanan cika Shekaru 60 da ‘yanci kai Buhari ya tabbatar da tabarbarewar tattalin arziki da tsaro a Najeriya

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanar da cewa kasar nan tana cikin halin tabarbarewar tattalin arziki

Advertisements
Advertisements

Ya kara da bayyana cewa, akwai manyan kalubale da kasar nan ke fuskanta na fannin tsaro a sassan kasar nan

Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a yayin jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar cikar kasar shekaru 60 da samun ‘yancin kai A ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki.

Ya ce hakan kuwa daidai yake da kowacce kasa domin kuwa dukkan duniya ne ake cikin wannan halin.

Buhari ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga ‘yan Najeriya a ranar da kasar ta cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai.

  Wasu 'yan fashi sun bayyana dalilinsu na kwamushe kudaden mutane

Shugaban kasar ya kara da amincewa da cewa, kasar na fuskantar matsalolin tsaro daban-daban a sassan kasar.

Ya ce, “A yau na tabbatar da cewa Najeriya tana cikin mawuyacin hali na tattalin azriki kuma hakan ce ta kasance ga kowacce kasa a fadin duniya. Muna fuskantar kalubalen tsaro a sassa daban-daban na kasar nan.”

A wani labari na daban, kungiyar Igbo for President Solidarity Congress (IPSC), wata kungiya ce a kudu maso yammacin Najeriya, ta tabbatar da bada hadin kai dari bisa dari akan shugabancin dan kudu maso gabas a shekarar 2023.

Ta ce yin hakan ne kadai zai kawo hadin kai a Najeriya. Shugaban kungiyar, Dr Olukayode OshinAriyo ne yayi wannan kiran a ranar Talata, 29 ga watan Satumba a Ibadan, jihar Oyo.

  Under Buhari, the country's golden years will return, says APC

IPSC ta ce kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya nuna, kudu maso gabas suna da damar rike kujerar shugabancin kasar Najeriya.