Bacin rai: Ta gutsire masa mazakunta da hakori

Rikici ya kaure tsakanin Abraham Musonda (52) da matarsa mai shekaru 40, sakamakon gaza cire mata bera da ta gani a kusa da gadonta

Advertisements
Advertisements

A tsakiyar rikicin ne, matar mai suna Mukupa ta fusata, ta sa hakori ta gutsirewa mijin na ta mazakuta, saboda gaza cire mata beran

A cewar jaridar Metro UK, an garzaya da Mr Musonda asibitin Kitwe, domin ba shi agajin gaggawa Rikici ya kaure tsakanin Abraham Musonda (52) da matarsa mai shekaru 40, sakamakon gaza cire mata bera da ta gani a kusa da gadonta, a gidansu da ke garin Kitwe, kasar Zimbabwe.

A tsakiyar rikicin ne, matar mai suna Mukupa ta fusata, ta sa hakori ta gutsirewa mijin na ta mazakuta, saboda gaza cire mata beran, a cewar rundunar ‘yan sanda.

  Tagwaye Sun auri Tagwaye sun kuma haifi Tagwaye a rana daya

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa matar ta yi ikirarin beran yana takura mata tare da hanata rawan gaban hantsi, musamman lokacin da ta dawo daki ta same shi a gefen gadonta.

Duk wani kokarinta na yin bacci a wannan dare ya gagara, sakamakon guje gujen da beran ke yi a cikin dakin, lamarin da ya tilasta ta kiran mijin nata, don ya fitar da shi, a cewar ta.

Amma da mijin ya ki amincewa da wannan bukata, sai Mukupa ta samu damar kafa hakoranta a mazakutarsa, lamarin da ya jawo ya samu rauni mai muni.

Bothwell Namuswa, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na shiyyar Copperbelt, ya shaidawa manema labarai cewa ma’auratan sun rabu, amma suna zama a gida daya, daki daban daban.

  Manyan Kano da kungiyar MURIC sun yabi zabin Ganduje akan Abdul-Jabbar

A cewar jaridar Metro UK, an garzaya da Mr Musonda asibitin Kitwe, domin ba shi agajin gaggawa kan wannan mummunan al’amari.