Atiku Abubakar yayi kakkausan tsokaci akan abinda ya faru a Jos

Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da kisan da akai wa musulmai a Jos

Advertisements
Advertisements

Atiku ya kuma roki yan Najeriya da su bada gudummuwarsu wajen taimakawa jami’an tsaro su samu nasara

Ya yi jimami da kuma ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayuwarsu tare da fatan samun rahamar Allah

Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da kisan matafiya a Jos da sauran kashe-kashen da ake a sassan Najeriya, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Aƙalla mutum 23 aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 23 suka jikkata a kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta arewa ranar Asabar da safe.

Atiku ya roki yan Najeriya da su baiwa jami’an tsaro haɗin kai domin su fuskanci wannan yaƙin kuma su samu nasara.

  Workers Salary Adjustment by Some Nigerian Governors Without Considering About the Economic Challenges

Gwamnati ta kara zage dantse

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kara zage dantse da jajircewa domin dawo da zaman lafiya a faɗin kasar nan.

A jawabin da kakakinsa, Paul Ibe, ya fitar, Alhaji Atiku yace:

“A yanayin halin da kasar mu ta shiga na rashin tsaro, jami’an tsaro na iyakar bakin kokarinsu.”

“Amma idan irin waɗannan abubuwan suna faruwa da kuma raɗaɗin dake biyo bayansa zai sa muji kamar ba ayi komai ba.”

Atiku ya mika ta’aziyyarsa ga wadanda lamarin ya shafa

Tsohon mataimakin shugaban ya yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda aka kashe tare da nuna damuwarsa kan yadda suka haɗu da ajalinsu cikin mummunar yanayi.

  Rundunar sojojin saman Najeriya sun kashe 'yan ta'addan ISWAP yau

Ya kuma yi Addu’a tare da fatan Allah ya kawo karshen halin da Najeriya take ciki kuma ya gafartawa mutanen da aka kashe.

Malamai biyu da ɗalibi ɗaya daga cikin waɗanda aka sace a kwalejin noma dake Bakura, jihar Zamfara sun tsero daga hannun yan bindiga, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mataimakin shugaban kwalejin, Ali Atiku , shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin.

Yace hukumar makaranta ta gano cewa maharan sun yi awon gaba da ɗalibai 15 da kuma malamai guda uku.