Apostle Paul Yace Wani Gwamna Mai Ci Zai Mutu

Apostle Paul Okikijesu na cocin Christ Apostolic Miracle Ministry ya yi hasashen abubuwan da yayi ikirarin za su faru a 2021

Advertisements
Advertisements

Shugaban addinin ya yi ikirari cewa wasu gagaruman abubuwa za su wakana a siyasan Najeriya

  • Okikijesu ya fada ma jama’a dalilin da yasa akwai bukatar su yi wa kujerar mulkin Najeriya addu’a

Wani Shugaban addini, Apostle Paul Okikijesu na cocin Christ Apostolic Miracle Ministry ya yi ikirarin cewa Allah ya bayyana masa cewa wani gwamnan Najeriya zai mutu a 2021.

Okikijesu wanda yayi ikirarin a wani wahayi da ya saki na sabuwar shekaara ya ce mutuwar gwamnan namiji zai ba mace damar zama gwamna.

Haka Ubangiji ya fadi: Wata mace za ta zama Gwamna kwanan nan. Wani gwamna namiji zai mutu kuma mataimakiyarsa wace take mace za ta dare kujerarsa a matsayin gwamna.

Haka Ubangiji ya ce: Za su amince ccewa mace wacce ta kasance mataimakiyar gwamna ta zama gwamnan wucin gadi. Zai zama kamar irin lamarin Jonathan da Yar’adua.

Sai dai malamin bai bayyana jihar Najeriya da hasashensa zai fada a kai ba.

Ya kuma yi ikirarin cwa Allah ya bayyana masa cewa za a yi gagarumin rikici a Aso Rock.

A cewarsa, rikcin zai jijjiga kasar gaba daya kuma zai shafi duk wani ruhi da ke kasar.

Ubangiji ya fadi cewa: Wani gagarumin rikici zai barke a Aso Rock tsakanin Janairu da Maris 2021. Zai bazu sosai; zai girgiza kasar sannan ya sa mutane rawar jiki.

Ya bayyana cewa rikicin da zai faru a fadar Shugaban kasa zai sanya mutane cikin damuwa. Malamin ya bukaci al’umman kasar da su yiwa Aso Rock addu’a.

Ya soki maganganin cewa idan aka baiwa wani sashen kasar nan mulki zasu yi kokarin ballewa daga kasar.

Ya jaddada cewa akwai bukatar nuna adalci, saboda mayar da wani bangare saniyar ware ya sa suke neman ballewa daga kasa.

  Atiku Abubakar yayi kakkausan tsokaci akan abinda ya faru a Jos