Amarya ta mutu a ranar aurenta a karamar hukumar Funtua-Katsina

Amarya Fatima Hassan Fari, wata budurwa a karamar hukumar Funtua ta Jihar Katsina da mutu awanni uku kafin daura mata aure

Amarya Fatima Hassan Fari, wata budurwa a karamar hukumar Funtua ta Jihar Katsina da mutu awanni uku kafin daura mata aure

Advertisements
Advertisements

Ta mutu ne misalin karfe 7 na safiyar ranar Asabar 2 ga watan Janairun 2021 a lokacin da ake shirin daura mata aura karfe 10 na safe

Yan uwa da abokan arziki sun yi alhinin rasuwarta tare da bayyana halayenta na kirki a shafukan dandalin sada zumunta.

Wata budurwa a ake shirin daurawa aure, Fatima Hassan Fari ta rasu a ranar da za a daura mata aure a karamar hukumar Funtua da ke Jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa Fatima ta rasu ne misalin karfe 7 na safiyar ranar Asabar 2 ga watan Janairun 2021, awanni uku kafin daura mata aure da aka yi shirin yi karfe 10 na safe.

An yi mata jana’iza misalin karfe 2 na ranar Asabar din bisa koyarwar addinin musulunci.

Kawayenta, da ‘yan uwa da sauran abokan arziki sun yi alhinin rashin ta a shafukan dandalin sada zumunta na Facebook.

Related Post

Wani abokin karatunta, Mallam Muhammad Sani Isah ya bayyana marigayiya Fatima a matsayin mace mai halaye na gari tare da taimako da jin kan al’umma.

“Ina bankwana da abokiyar karatu na Fatima Hassan Fari, wadda ta riga mu gidan gaskiya safiyar yau zuwa aljanna inda za ta hadu da mahaifinta,” kamar yadda ya rubuta.

“Innallahi wainnailaihirajiun Fatima ta rabu da mu, Allah SWT ya yafe mata kura-kurenta ya saka mata bisa ayyukan alherin da ta yi da Jannatul Firdaus.

Ina mika ta’aziyya ta ga yan uwanta musamman mambobin Asacosa. Allah ya basu hakurin jure wannan babban rashin.”

Sani Isah ya kuma bayyana wasu kyawawan halayenta da gaskiya da jin kan al’umma da aikata abinda ya dace koda kowa yana sabawa.