Alkalan wasan sun sha shegen duka a hannun yan wasa a fili

Alkalan wasa a Ghana sunsha dan karen kashi a yayin da suke gudanar da alkalancin wasa na kasa da kwararru na kasar.

Advertisements
Advertisements

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa a kasar Ghana sun lakadawa alkalan wasa duka har sun cire wa wani hakori

Lamarin ya faru ne bayan an buga wasa tsakanin kungiyar Wanamafo Mighty Royals da Bofoakwa Tano a ranar 28 ga watan Maris.

Magoya bayan kungiyar da aka buga wasan a gidansu ba su gamsu da yadda alkalin ya hura wasan ba hakan yasa suka far masa bayan an tashi.

Fusatattun yan kallo sun lakadawa alkalan wasan kwallo duka a gasar wasar Division One a wasan da aka buga a mako na 14 a ranar Lahadi 28 ga watan Maris, LIB ta ruwaito.

A cewar kafafen watsa labarai na kasar Ghana, lamarin ya faru ne bayan da kungiyar Wanamafo Mighty Royals suka buga wasa da Bofoakwa Tano aka tashi wasan ba tare da an saka kwallo a ragar kowa ba.

Rahoton ya ce magoya bayan kungiyar da aka buga wasan a gidanta sun afka cikin filin bayan an hura usur din tashi suka lakadawa jami’an wasan duka har ta kai ga rafari Niatire Suntuo Aziz ya rasa wasu daga cikin hakoransa.

A cewar Starr FM, maso kungiyar a gidanta ba su gamsu da yadda alkalin wasan ya yi aikinsa ba hakan yasa suka far masa da duka.

Kamar yadda hotunan ya nuna, alkalan sun fita hayyacinsu sakamakon harin da yan kallon suka kai musu bayan wasan.