Adebiyi Ya Sanar da Ranar Kammala Titin Abuja-Kaduna-Kano

Adebiyi ya bayyana cewa za a kammala titin Abuja-Kaduna-Kano kafin wa’adin wannan gwamnati ya kare inda ya ce an ci karfin aikin. 

Advertisements
Advertisements

Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke ziyarar duba aiki a Kano tare da tabbatar da cewa sun gamsu da ingancin aikin. 

Ya bawa al’umma hakuri kan yanayin aikin tare da shawartar dan kwangila da ya kara dagewa don kammaluwar aikin cikin lokaci. 

Mista Funso Adebiyi, Shugaban sashin Gini da Gyaran Manyan Tituna, Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, ya ce za a kammala aikin ginin titin Abuja-Kaduna-Kano kafin karshen shekarar 2023.

Adebiyi ne ya bayyana haka lokacin da ya ke duba ci gaban aikin a Kano ranar Jumaa. 

Aikin sake fasalin titin Abuja-Kaduna-Kano wanda ake ta samun cigaba za a kammala shi kafin wa’adin wannan gwamnati ya kare.

Mun gamsu da ingancin aikin kuma muna kokari muga an kara sauri a aikin.

Kuna iya ganin yadda aiki ke gudana a duka bangarorin titin mai nisan kilo mita 375 daga Abuja-Kaduna-Kano,a cewar sa.

Daraktan ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati a kokarin da ta ke na samar da ingantaccen aiki wanda za a dade ana mora.

Ya kuma roki masu amfani da titi da su ci gaba da hakuri da yanayin titi har zuwa lokacin da za a kammala aikin.

An samu ci gaba sosai. Saboda an kammala fiye da kilo mita dari duk da ba a jere ba, an kammala bangare na daya zuwa na uku (Abuja – Kano),a cewar sa.

Ya ce an kammala kilo mita 40 a bangare na biyu (Kaduna-Zaria), da kilo mita 70 karkashin bangare na uku (Zaria-Kano).

Adebiyi ya bayyana cewa za a kammala titin Abuja-Kaduna-Kano kafin wa’adin wannan gwamnati ya kare inda ya ce an ci karfin aikin

Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke ziyarar duba aiki a Kano tare da tabbatar da cewa sun gamsu da ingancin aikin

Ya bawa al’umma hakuri kan yanayin aikin tare da shawartar dan kwangila da ya kara dagewa don kammaluwar aikin cikin lokaci

Mista Funso Adebiyi, Shugaban sashin Gini da Gyaran Manyan Tituna, Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, ya ce za a kammala aikin ginin titin Abuja-Kaduna-Kano kafin karshen shekarar 2023.

Adebiyi ne ya bayyana haka lokacin da ya ke duba ci gaban aikin a Kano ranar Juma’a. 

Abuja-Kaduna-Kano wanda ake ta samun cigaba za a kammala shi kafin wa’adin wannan gwamnati ya kare.

Mun gamsu da ingancin aikin kuma muna kokari muga an kara sauri a aikin.

Kuna iya ganin yadda aiki ke gudana a duka bangarorin titin mai nisan kilo mita 375 daga Abuja-Kaduna-Kano,a cewar sa.

Daraktan ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati a kokarin da ta ke na samar da ingantaccen aiki wanda za a dade ana mora.

Ya kuma roki masu amfani da titi da su ci gaba da hakuri da yanayin titi har zuwa lokacin da za a kammala aikin.

An samu ci gaba sosai. Saboda an kammala fiye da kilo mita dari duk da ba a jere ba, an kammala bangare na daya zuwa na uku (Abuja – Kano), a cewar sa.

Ya ce an kammala kilo mita 40 a bangare na biyu (Kaduna-Zaria), da kilo mita 70 karkashin bangare na uku (Zaria-Kano).

Kuma ana kan kammala bangarori da dama na titin, ana kuma cike guraren da ke da bukatar gyara don saukakawa masu bin titin.

Yana da kyau in gyara furucin masu cewa aiki baya tafiya.

Muna aiki tukuru don ganin mun kammala aikin lokacin da aka diba tare da yin ingantaccen aiki, kamar yadda ya bayyana.

Ya kuma bukaci dan kwangilar da ya kara sauri da kuma diban karin ma’aikata don kammaluwar duka bangarorin titin.

  Wani Jajirtaccen Dan Najeriya Ya Kirkiri Kafar Yanar Gizo Gizo Saboda Rage Zaman Banza