Abdul-Jabbar Nasiru Kabara makaryaci ne inji Ganduje

Abdul-Jabbar Nasiru Kabara ya tabbata makaryaci kuma mayaudari, inji Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yana kuma mai musanta ikirarin malamin na cewa Kwamishinan Ilimin jihar ya tabbatar da zaluntar sa.

Advertisements
Advertisements

Jim kadan da dakatar da shi daga gabatar da wa’azi da huduba, Abdul-Jabbar ya shaida wa manema labarai cewa, an yi hira da Kwaminishin Ilimin Jihar Kano wanda ya tabbatar da cewa, an zalunci malamin a cewarsa.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, a halin yanzu gwamnatin Kano wadda ta gana da Majalisar Malaman Jihar, ta bukaci malaman da su duba ayoyin Al-Kur’ani da Hadisan Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam don fitar da hukuncin da ya dace kan Abdul-Jabbar.

  Tirkashi! Anyi dumu-dumu da wani ango tare da kawar amarya a ranar biki

Dakataccen malamin ya bayyana cewa, malaman jihar Kano sun shigar da siyasa a cikin addinin Musulunci.

Tuni Jami’an tsaro suka killace gidansa da masallacinsa na Ashabul-Kahfi, sannan kuma aka yi masa daurin talala.